AUREN JINYA COMPLETE HAUSA NOVEL

AURAN JINYA COMPLETE HAUSA NOVEL.

Page:01 Auren jinya, auren jinya ubangiji ya tsarini da yin auren jinya, duk wanna kyawo nawa da komi nawa, na taso gidan talauci sannan na Kare kan yin auren jinya, Ihu da sowa dukan yan matan da samarin sunka duka, wani saurayi Dan baki ya dura da cewa shigiya nana. Samari ne da yam mata ke zaune cikin wata inuwa , a cikin wata makaranta, waton sokoto poly. Babu abinda sukeyi sai firar duniya. Wadda akan kira da Suna Nana, kallo daya zaka yimata kasan cewa kyakyawa ce a cikin kyawawa, Sannan ga tsantsan wayewa ta yan Matan zamani, ko a fanni suturarta zaka san cewa tana cikin zamani kuma duniya ta aure ta. Haba haba AI yanzu mata sunyi wayo Sun daina auren jinya, ina laifi ka samu wanda ya kama karatunsa ya fara aiki ko kasuwanci kudi na shigowa ta ko ina sai kuyi auren babu wata wahala, shan dadi kawai zaku rigayi.’ Kisa duk kalar supar da kikeson, ki Saka kalar less dinda ke ke so, ki hau babba mota, ki zagi duk ubanda kike so ba Mai Yimiki magana. amma inah ni , ina wani auren jiya kullum cikin fargabar abin yin lalura da abinda mutum zai ci, Kai auren jinya baiyiba. Dariya dukansu suka saka, sunka ci gaba da saurarin hadisan nana na yam mata su daina yin auren jinya, wanda zuwa yanzu duk wata kawa ko aboki yasan karatun nana. Wani saurayi Na gani zaune kusa da majalisar su nana tun farkon Zamansu , Sai dai ga dukan alama saurayin bako ne kuma baya cikin yan zaman majalisar. Amma dukan firarsu bisa kunninsa suke, iya tunaninsa ya rasa wani irin aure ne, ake kira da auren jinya, haka kawai zurciyarsa ta kwadaita masa son kullah wata alaka da nana domin jin maanar auren jinya. Sai dai yana ganin ba karamar wahala zai sha kafin yama nana ta saurareshi saboda ya riga da ya hango inba ‘yayan banki ga rika ba to bakada wani mutumci a idon nana, kuma shikam baida ko asi. Can yaji nana ta ci gaba da biyan karatun ta, kee sani zainab nifa ko tsoho na samu indai ba auren jinya zanyi ba to banda matsala, sake bugewa sunkayi da dariya Wanda akan kira zainab ta ce to aiki yaro ba kudi shine tsoho, tsoho da kudi ai yaro ne, shegiya zainab dadina da ke kinsan kan abin, cewar nana. nifa iya kata da saurayi indai naga yanada dan wani abu in yazo yana sona zan ce ina sonsa amma fa cikin zurciyata ba da Gaskiya nakeyi ba, kawai zan wanki gara, amma aure kam sai mai kudi, cewar zainab. Kokam Allah ya shiyarku cewar wata budurwa kyaukyawa ta karshe mai kalar indiyawa amma kallo daya Zaka yimata kasan bafillatana ce, saboda Tsananin kyawonta idan ka kallah sau daya gabanka ya fade domin zaka yi tunanin gamu kayi.’ Don Allah rufamuna baki cewar nana, ta katse budurwar mai suna meenatu , Ai gara mu da muna fadi raayinmu amma ke saboda tsabar munafucci Duk wanda Yazo korarsa kikeyi sannan in anyi magana kice muji Tsoron Allah da ke muke jin tsoro. Meenatu murmushi tayi saida fararin hakoranta sunka baiyana ta ce kome dai zaki ce ke ce, banga Wanda yayimin ba ne IN nasamu zanyi Auren insha Allahu. Nifa nana nafi son saurayi bisa ga babban mutum, koda ko baida ko sisi muddin dai yanada ilmi da yar Sana’a yadda cikin rufin asiri zai duke dawainiyar iyalinsa, shifa arziki da samu duka suna wajin Allah kuma sai ya so zai baiwa wanda ya ga dama alokacinda ya so. Nidai tashi Muje gida cewar meenatu ko dai yanzu mun dan huta. Hakane kawata wlh yau garin ana balain zafi cewar nana, sallama sunkawa sauran abokanin karatunsu da kuma firarsu.

Page3 Taba ka lasa, yaro ne Matashi Mai jin she wani ne saka makun tsabar baiwar da Allah yayi masa da kyau, sannan gargado yanada dan kudinsa. Amma fa karyarda a azama ma kansa tayi yawa domin in munyi laakari da yadda yake kashe kudi zakayi mamakin ina yake samunsu, Amma da sannu mai karatu zai fahimta . Faisal a ainihin sunan sa abukaninsa da yam matanda yake hudda da su ne sunka saka mishi wannan suna taba ka lasa, domin Allah ya aza mishi jarabar son mata kuma duk budurwar da ya kyalla ido ya gani, ya ji tayimasa zai yi iya yinsa yaga ya samita ya biya bukatarsa, Sai yayi gaba. Yau ma kamar kullum nana ce tare da meenatu hanyarsu ta zuwa kasuwa siyayya, Sai kuma akayi rashin Sa’a ana zananin zafin rana, kuma ga rashin abin hawa. Sunfi minti talatin suna jiran abin hawa, meenatu ta kalli nana ta ce ina ganin fa nana yau bamu fito a sa’a ba, kalli tun dazu muke jiran abin hawa mun kasa samu. Wai ko hakura zamuyi da xuwan kasuwar cewar meenatu tana kallon Nana. Haba meenatu ke na ganin tafiyar zata fasu duk wahalarda munka sha, gaskiya mu dai kara jira Inji Nana. Shikenan ai mai rabon shan duka baya ji sai yasha in ji meenatu. Wata mota sun kaga tayi faking kusa dasu, wani saurayi mai matukar kyawa sun ka gani, cikin muryarsa da ya saba yudara yam mata, yayi musu sallama. Nana ce ta amsa cikin yanga da jin aji domin kallo daya tayi masa ta ga tasamu irin mijin da take mafalkin samu , domin ko baa fadamata ba tasan mai kudi ne ko dan mai kydi, uwa uba kuma yaro matashi mai kyau. Koda ita a rayuwarta bada damu da ko ya mutum ya ke ba muddin yana da yayan banki, lokaci guda tana rokon Allah yasa ba dan meenatu ya tsaya ba, domin some times hakan yasha faruwa sai ta san ranta da mutun karshe ya ce meenatu yake so. Ita ko meenatu tayi masa korai kare ayi biyu babu bata dashi meenatu batadashi. Yam mata adon gari ina zuwa cikin wannan rana ya fada yana kallon meenatu Wanda ita ko samma hankalinta bayama kansa. Yam mata ina magana cewar saurayin yana kokarin jawo hankalin meenatu gunsa. Malam kurma ce cewar nana domin samun mafita da cikar burinta, ikon Allah saurayin ya fada cike da jimami, sannan ya meda kallonsa izowa ga nana yana cewa yam mata ina kunka nufa in ajeku domin ni ban cika son ganin kyawawa nasha rana ba. Cikin dan basarwa nana ta ce kasuwa zamuje motar mu ce tasamu matsala. Salin halin nana da meenatu tayi baisa ta mamaki ba asali ma cigaba tayi da kallon abibin hawa da ke wu cewa, amma cikin ranta tana mamakin Irin halin nana. Domin yau in tayi tsammaninta nan gobe zata wuce sanin ta, shiyasa bata da tabbas ga nana, abinda kawai tasani nana na mugun sonta sannan abin Nana nata ne. Taba taji nana tayi alamun maganar kurami tana nuna mata da ta shiga mota, ba karamin dariya abin ya bata ba yadda nana ta meda ta kurma lokaci guda.

Page5 Kasan cewar mummy meenatu ma aikaciyar gwannati ce , Time den da suka iso gida, tana wajan aiki. Dakin meenatu suka baje kayan da suka sayo, nan nana ta kama fitar wa meenatu nata, komi iri daya ne ita meenatu. Anko ne na wata kawarsu zatayi aure, sai sarka da yan kunne da abin hannu sai takalma da jaka da mayafi, duka kalar da zata yima ankon dai dai. Kayan ba karamin burge meenatu sunkayi ba, ta kalli nana gaskiya kayan sunyi kyau, idan Kin batama mutum kisan yanda zaki faranta mishi. Dariya nana tayi tace, ai kedin ce meenatu sai da zafi wallahi, Amma kafin ke yabamin ke Fara us bawa mummy itada da ta bada kudin siyayyar. Zaki fara ko nana kesan mummy ta sha fadamiki duk abinda tayimin zata iya yimiki domin kema ‘ya ce a wajanta. Hakane meenatu kuma na tabbata domin duk abinda uwa kewa diyarta mummy nayimin, Fatana Allah ya bani abin sakamata. Yanzu dai ga kudinda faisal ya bamu , bare muraba na dauki nawa na baki naki yar kurma, cewar nana cikin zulayar meenatu. Harara meenatu ta aikama nana kisan wallahi zan rusa duk wani shirinki in kinka Kuma kirana da kurma. Kuma maganar kudin ki barsu kinfi kowa sanin banda abinda zanyi da kudin, lokaci guda annurin fuskar nana ya gushe ta kalli meenatu ido cikin ido me kike nufi meenatu. Allah dolenki ke duki naki kaso ko ai kati kena sawa, ita ma meenatu kallon Nana ta keyi, kisan fa mummy kesakamin kati kebar kudin kawai nana, nifa da asun ran na ne dama baki amshi wannan kudin ba. Nasani meenatu shiyasa ma na rufe bakinki tun farko, kuma dolenki ki karbe naki rabon ko kuma wallahi muyita. Murmushi meenatu tayi tare da dafa kafadar nana naji zan amsa, amma kije da kudin daga baya zan karba Kada mummy ta gansu sannan ko inbata labarin inda kika samesu. Alamun tsoro ya baiyana a fuskar nana, domin duk tsiwarta tana tsoron mummy tare da mugun jin kunyar ta bata kaunar tayima mummy laifin da zata yima mata fada. Meenatu kallo nana tayi tana dan murmushinta, alamun samun nasara rashin amsar kudin. Ta shi muje na rakkaki tun kafin mummy ta dawo, ba musu nana ta meki tare da dukar ledar kayanda suka yi siyayya. Suna tafiya suna dan taba firarsu har sunka kai wajanda yakamata meenatu ta koma gida. Sallama sukawa juna, meenatu ta juya zuwa gida, nana ma tayi gidansu. Faisal ko tunanin yadda zai ci nasara kan nana ya shiga yi, bayan ya koma gida, tabbas yasan ba wata wahala zai sha ba idan yayi la’ akari da yadda ta sake jiki dashi haduwar farko. Kuma a hanginsa sai tayi sun kudi Dan haka ya ke ganin abu ne mai sauki cimma gurinsa.

Page6 Wayarsa ya jawo ya diling numbar nana da yayi seven, kirrrr kirrr yaji kiran ya shiga , Amma ga mamkinsa har wayar ta katse baa duka ba. Sake kiran yayi cikin sa’a lokacin nana ta fito daga wanka sai ta dauki wayar, tare dayin sallama gimbiya nana barka da maraice cewar faisal. Ranka ya dade ya yau ya kuma gajiyar dauwainiyar mu cewar nana. Haba wace dawainiya gimbiyar mata, dama ina son rokon wata alfarma ce a gariki? Ke bani adress den ki na kawo miki ziyara har gida, da fatar zan samu wanna arxikin? Murmusawa tayi kamar yana ganinta sannan tace haba faisal ai ka wuce wannan guna bare kawai in mun gama wayar zan turuma yanzu. Godiya ya fara yimata kamar Wanda ta wa wani kyauta. Kasan Cewar ya San kan mata ya dade yana mu’amala dasu Cikin minti biyu ya ja nana da dan fira, tanan yake tambayarta kawarta kurma, ta ce masa yanzo ma sunka rabu, daga karshe sunkayi sallama. Cikin mintuna biyu nana ta turamasa adress den ta, tare da Dan neman guri aranta, na in yashigo hannunta yadda Zara rika yankansa. Ameer tun ranar da yaga meenatu yaji ta kwanta mishi a rai, sai dai yana jin tsoron kada ta kasan ce halinta daya da nana. Amma duk da Haka Zai jaraba sa’arshi ko Allah zaisa ya dace. Wanka yayi yasamu kayansa masu yar dama ya saka , haka ma ta gifin takalma suma masu dama ya nema ya saka. Bai wata shan wahala ba wajin gane gidansu meenatu domin ranar farko da ya gansu a skull ya biyo su domin sanin gidan. Yana xuwa bakin Gidan zurciyarsa ta soma harbawa, karon farko kenan a rayuwar ameer zuwa gidan budurwa da sunan zuwa nemanta. Cikin sa ‘a ya sami wata yar majalisar samari kusan gidan, nan da nan wata shawara ta fadu mishi garansa, dole ya samu kusanci da daya daga cikin samarin. Ne!sa da su ya samu ya zauna amma dukan firansu yana ji koma yana fahimtar kowa cikin yan majalisar, nan ne ya fahimci akwai mai wanki da goga cikin yan majalisar, kuma ya fahimci dan cin rani ne daga kauye, haya yakeyi. Bai wani jimawa ba akazo karba wanki wajan mai wanki, shima cikin hikima yabi mai wankin daga baya domin yaga shagunsa. Cikin sa’a shagon na Mai wankin baida nisa da gidan su meenatu. Yana kallo mai wankin ya bude shagonsa ya ba masu karba wankin, kayansu , sallama yawa mai wankin tare da mekamishi hannu, cikin mutumci shema mai wankin ya mekama ameer hannu sunka gaisa . Don Allah malam neman taimako nakeyi gunka cewar ameer, lokaci guda mai wankin ya meda dukan hankalinsa gun ameer. Ina jinka malam Allah yasa inada ikon taimaka maka, cewar Mai wanki, shema ameer meda dukan hankalinsa yayi gun mai wanki. Don Allah malam wajan zama nake nema na haya ne mutumin kauye ne nazo bida, kuma gashi cikin rashin sa’a ban san kowa ba garin. Kallo tausayi mai wankin yayi masa, yace insha allahu ka samu masauki , Kai har aiki ma inajin ka samu idan har bai yima kadan ba, domin ina neman yaron da zai ringa taimakamin sai kuma gaka Allah ya kadumin. Fuskar ameer ta nuna tsantsan farin cikinsa, godiya ya fara zubama mai wankin, sannan ya fadama mai wankin zaije ya doko kayansa wajanda ya fara sauka.

PAGE: 08* ” Hmm nidai har kullum ina nuna miki illar wasu mazan dan wlhy….”, kafin Meenatu ta k’arasa zancen ta tuni Nana ta katseta tana cewa” kinga ni ya isheni haka, nasan fa halinki sarai yanzu kin kama ma mutum wa’azin nan naki, bansan me maza suka miki ba”, Murmushin tak’aici Meenatu tayi dan tana jin tak’aicin irin wannan hali na k’awarta, ” Naji to na kyaleki bazanyi miki wa’azi ba tunda bakison a fad’a miki gaskiya”, cewar Meenatu, ” Ba wai gaskiya ce banso ba, a,a gani nayi ina laifin Faisal dan Allah ya nuna yana sona kuma nima irin mazan da nakeso ne, to shikenan sai inyi rejecting tayin da yayi min, a,a wlhy ina son abina”, ” Ok to Allah ya kyauta ni kinga zan shige class zaki zo muje ko kuwa jiran masoyin naki zakiyi?, ” Tabb jeki kawai bazan shiga ba jiran Faisal d’ina nakeyi, kawai sai mun had’u”, Meenatu wucewa tayi ba tare da ta sake cewa komai ba, a ranta cewa take Allah yasa ki gane gaskiya ki daina irin wannan halin, ace mutum ba kamun kai ko d’aya a matsayinki na mace mai daraja. Umar bai bar skull din ba saida yaga shigar meenatu class sannan yaga fitar nana da faisal a mota, kaitsaye ogansa ya kira ya shaidamishi duk wani abu da yasashi nema ya hadu , ina zai ganshi ya bashi kayanda yasashi nema. A wani gidansa na hutawa suka hadu , yayi bayan tun fituwar meenatu daga gida ita nana har kawo warsu skull har fitar nana skull den da shigar meenatu Class. cikin kalilan lokaci ameer ya gama shirinsa ya badda kama kamar yarda ya saba, ya tasar unguwarsu meenatu. Mashin ya samu ya kaishe bai ajishi ko ina ba sai bakin shagon mai wankin, cikin saa ya samu mai wanki, sallama yayiwa mai wankin, bayan ya amsa ya bashi ixinin shuguwa cikin shagon, ya nuna mishi inda zai aje kayansa, bayan ya aje Sannan mai wankin ya fadamishi sunansa garbati inda ya tambayi ameer sunansa, lokaci guda sunan tanko ya fadumishi arai batare da wata shawara ba ya furta tanko , shema garbati sai da sunan ameer ya bashi dariya, baisan sadda ya furta tanko shin? tanko mai kan cin bashi cewar garbati ya fada yana dariya, sannan ya kara da tanko da garbati a shagon wanki, shima dai ameer dariya sunan nasu ya bashi baisan lokacinda ya dara ba, nan take ya gane garbati mutum ne wanda ya cika Sun ba’a, da zulaya. Nan ya dan kalli garbati shema cikin siffar xulaya ya ce kasan fa, tunda kai oga na ne bazan rika kiran sunanka ba , zan rika kiranka da oga garbati ko oga kawai. Shema garbati kallo ameee yayi yace, ah ah tanko kada kesa in rika jina wani babba, don Allah kerani da sunana kawai garbati. Cikin lokaci kankani ameer ya fara sanin halin garbati cikin ‘yar wannan firar da sukeyi, inda ya fahimci garbati mutumin kirki ne, sannan bai duke kansa bakin komi ba, lokaci guda, ameer yayi niyar taimaka mishi, domin ya fahimci garbati yana cikin irin mutanenda inda Allah yayi su masu kudi, tabbas al ‘umma zasu amfana da dukiyarsu. Cikin lokaci kadan shagon garbati ya soma cika da samari , nan ameer ya fahimci nan ma wajen firar matasan anguwar ne, duk Wanda yaxo shagon fira ko amsar wanki ko kawo wanki sai garbati ya gabatarda ameer gunsa, inda yake cewa ga dan uwansa nan yaxo daga kauye, wannan abin da garbati keyi yasa ameer kara ganin kemarsa, a idonsa. Duk firanda Sukeyi su Garbati iyakar ameer dan murmusawa kasan cewarsa mutum ne Wanda bai cika dariya ba da yawan surutu. Tun lokacinda ya ga Time din tasowar yan poly tayi ya fara baza ido domin cikin bincikenda umar yayi masa ya nuna mishi tanan ne suke bi in zasu skull , kuma tanan suke bi in zasu dawo, karshe ma ba wata hanya ta fitarsu sai ta hanyar shagon garbati, Baa fi minti ishirin ba sai ga meenatu cikin dan adaidata ya sauketa, cikin shigarta ta kamala kamar kullum. Tun kafin ta fito a dai daitar ta biya mai motar kudinsa , ta gabansu ta biyo zata wuce ga mamakin ameer sai yaga garbati na kallonta yana dariya, tare da yimata barka da dawowa harda tambayarta mahaifiyarta, cikin mutunci sunka gaisa sannan ta wuce. Cikin wa yanda ke zaune wani mutumin ya fara cigumin meenatu , yace ga yarinya dai dai aure amma ta kasa fidda mijin aure, duk yadda kuke mutumci da ita da kayimata maganar aure zata rufe ido ta cema mutumci. Wani yace ai dakaga macce mai kyau dole sai tayi ruwan ido, ba mamaki wani mai mugun kudi take jira, wani kuma saurin katse su yayi , yace wlh banda meenatu domin kudin mutum baya gabanta itadai ta tsani maza, da dai kawarta ka ce da wannan kam kowa yasan mai kudi take jira. Wani kuma cewa yayi ai da ganin kyawon wannan yarinyar kasan dole tabada aljannu, haka dai fira ta kasance har lokacinda kowa ya kama gabansa saboda kawowar magariba. Sai alokacin faisal ya aje nana, tare da manyan ledodi, komi ya faru a idon ameer, abin ba karamin bashi haushi yayi ba, itama nana kamar meenatu saida ta gaisa da garbati sannan ta wuce . Tare sunka je sallah magariba tare sunka dawo, alamun shiguwar sako yaji cikin yar karamar wayarsa ameer, saida sunka zauna sannan ya samu damar duba sakon, umar ne ya turumishi sako, kamar haka, Sallama ranka ya dade, ya bakunta? gaskiya ranka yadade hankalina ya kasa kwanciya na zamanka wanna shagon, akwai hanyoyi da yawa na neman soyayyar meenatu basai kasa kanka wannan aiki ba. Murmushi ameer yayi, sannan ya turamishi amsa kamar haka, Wasallam kada kadamu nasan mi nakeyi , zan kira xuwa gobe idan da yuwuwar haka.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *