Home Novels Auran kinsan wuta page 7

Auran kinsan wuta page 7

2
0

Koda alhaji usman yatafi, yarake subiyu wani irin kalo Jamila takwashe dan liti dashi, tace amma kai kam anyi mayan son kudi, saboda kwadayi abun duniya shiyasa kana yaronka dakai, Ka abince aure na na sati uku, hnmmmm yanzuma intambaye ka, kasan me akecewa in anje tadi? Dan liti dayayi tsaye yana kallonta, yagirgiza mata Kai alaman besani ba, tace kaga illan talaka ko ga kwadayi ga dakikanci, dan liti shi dai yazuba mata ido yana kallonta, Tace to ina jinka bakazo zance bane? To fadi inajinka, dan liti dai yana tsaye yanade hannunshi a girji, yana mata wani irin kallo , wanda koni yar mutan Kagara, banace nasan fasaran wannan kalon ba” Haka jamila taci gaba da fada mishi magan ganun duk daya mata dadi, shi dai nashi ido, Jamila tace kadai san badade wa zanyi ba inmukayi aure ko, yace eh nasani tace nifa sati ukun da alhaji yadiba, yamin yawa gaskiya, Dame zaka rikeni nasan duk alhaji usman dindai shi zeyima komai, Kai saboda talauci shiyasa kayarda da auren kisan wuta ko? Dan liti yace a’a kawai dai, alhaji usman ne yanemi alfarma, kuma ya cancacci inmasa ne, shiyasa nayar da, Suna chin haka saiko ga malam, tai mishi sannu da zuwa, dan liti yaduka har kasa yagai sheshi, ai malam yaji dadi,ya amsa mishi cikin mutunci da jindadin gai suwan da yayi mai, Sabani wasu samari, basaba iyayen budurwa girmansu, kuma malam farat daya yaji yana son yaro, yakwanta mishi, tana ganin malam yashige tajuya tana shigewa gida, tana cikin tafi ne tace zaka iya tafiya, Sai wani lokacin shi dai dan liti dakallo yabita, abun ma dariya yaba shi, yajuya yatafi Dan liti besha wuyaba wurin neman auren, jamila saboda daga malam har inna, Sun yaba da tarbiyan shi da nagarta, ga kuma natsuwa, Koda malam yanemin dan liti yaturo magaba tansa, dan liti baban abokin sa musa yasama, yafada mishi yadda sukayi da malam, Malam tanko yace to madalla abu yayi kyau, Allah yasanya alkhairi, dan liti yace amin, dan liti yace ammafa abba bazawara ce, masha Allah, kakoyi koyi da ma’aikin Allah, Hakan yayi kyau, kuma nizan jagoranci al amarin, zamu je tare da kannaina, insha Allah, dan liti yayi godiya, Biki dai yakan kama, ansa rana sati biyu masu zuwa, kuma malam tanko baban musa, shine waliyin ango, Alhaji usman yagama komai yayima jamila setin akwati hankare da kaya, yayima dan liti shima seti goma, na fitan biki, Yakuma ba dan liti gidan da zasu zauna, chiki da parlon da toilet dakuma kitchen, yakuma chema su malam karsuyi komai, shizeyi mata duk abunda iyaye kema yaransu, Sukayi godiya. To ranadai bata karya sai dai uwar diya taji kunya, a yau ne dubban jama’a suka sheda daurin auren dan liti da jamila, akan tsadaki naira dubu goma, Dubu goman ma alhaji usman ne yace ga dubu goman, yabayar saboda iyayenta sunsan ango beda kudi, wankin mota yakeyi kawai, karsuzo suchiga wani tunane shiyasa yabada dubu goma, Ankai amarya gidanta, kowa yatafi tunda bazawara ce, koda tarake ita kadai bata damuba, hasalima tafison hakan saboda suna makale da juna da alhaji usman a waya, Yana kara jadda damata, karta yarda yace zeyi wani abu da ita, ita kuma in yafadi hakan sai taji ranta yabaci, Tace mishi ita ko mazan sunkare mezatayi da wannan yaron, ai dai arufe, jamila tana zaune a parlon, tamagaji da kuka tsabar Kuka har idonta yakunbura,, sai kawai taji ana bude kofa ganin dan liti, ne yasa tamike tsaye tahau masifa, Wai kai dame kake takama ne? Dazakama mutane wulakanci, inbanda wulakanci meye nafita kaki dawowa gida tunsafe, kuma kasan yaune wa’adin zamana a gidanka yazo karshi, Ai tanemanka a waya ba asamunka, tanayi tana murguda mai baki 😏 Batama lura da irin kallon dayake mata ba, sai zuma masa masifa takeyi, yanadai ta kallonta saida talafa dan kanta tayi shuru, se yabi ta gefenta yashige daki, Aiko jamila kaman jira takeyi, tamishi dakin tana ruwan bala’i, shidai Komai beceba, tace aidama matsalan talaka kenan, kamai rana shikuma yamaka dare, Sai girman kai ka iya Kai bakowan kowa ba, bakada ko sisi, mtswww fuuuuuuu tabar dakin takoma parlon, tadauki wayanta kiran iPhone 8 ” Takira alhaji usman yana dauka tafashe mishi da kuka, shikuma yabi yagigice yace meyafaru ne baby j, Taja majina tace ya yadawo yanzu, ai seyazabura kikace yadawo? Eh yadawo yanzu nan, yabaki sakin? A’a be baniba ko magana beminba, amma lallai yaron nan yanason yaja dani, yana inane? Yana daki, kinsan menake so dake baby j, karki kuskura yaron nan yataba minke pls, haba my man aini takace kaikadai, meze iya yimin, dan yaronnan habadai aini nawuce saninsa, Dan liti dake daki kwance a kan gado, duk yana jinta, amma kalmanta nakarshe, shiya harzuka shi, yamike har jijiyoyin kansa sunyi rada rada, saboda bacen rai ” Jamila tana cikin wayanta da alhaji usman, taji kaman daga sama an warce wayan, tajuyo a fusace da niyar rashin mutunci, amma ganin yanayin face din dan liti ta tsorata, saboda bata taba ganin shi a haka ba” Yau yazama mata kaman wani namijin zaki, Tace meye na ansan min wayana? Ko kallonta beyiba yabude wayan yacire sim card din yasa a baki yataune, ai jamila naganin haka, tayi chikin shi amma yana juyowa ai setaja burki, Ya watsar da taunanne sim card din, yajuya zuwa daki Jamila harda saurinta wurin binshi, tanazuwa dakin sai bata ganshiba, taji motsinshi a toilet, tayi saurin shiga dai dai shiganta dai dai yana jefa wayan, chikin ruwa” Jamila tasa hannu a kai 🙆🏻 Tace waiyo ni Allah na yajuya yafita, yabar ta nan, tafiddo ido waje 😳 Tabiyo shi parlon wai kai mekake ji dashi ne? Mekake takama dashi ne? Daga tai mako dama ance inkaga mutun a rana,to ka kara ingiza shi ciki, daga taimako menene mijina beyima ba? A rayuwa yamaka suntura yabaka kudi, ya baka muhalli, duk wannan bai maba sai kaci amana! wlh ninafi karfinka inma sokake kataba jikina, wlh jikina yafi karfin yaro karami irin ka, a zabure yamike, yanunata da yatsa, yace idan kikakara cemin Yaro wlh zannuna miki true color na, Jamila babu abinda take kallo sai kirjin shi, da kezuwa sama yadawo kasa saboda bacin rai, Nisanki ne? Yashiga daki ya kwaso kayanshi, jamila kawai ganinshi tayi da kaya, yada face yace ke dasauri ta dako rinannun idanunta, dauko maya finki kibiyo ni, Tace inbiyo ka ina? Inazaka kaini karab suka hada ido, setaji bakinta yagaza furta komai, kawai tamike tashiga daki ta dauko mayafinta, da kuma jakan hannu wanda acikine tazuba su ATM card dinta dadai sauran abun bukatunta” Tafito tasame shi a tsaye yana ganinta, yakama hanyan kofar gida, itama tabishi jamila tana fita taga me adaidaita najiransu, da kallo tabi dan liti, Shi kuma tagefen ido yake kallonta, yasaka jakanshi aciki yashiga, itadai jamila kallon shi kawai takeyi, beko juyo yakalleta ba, yace inkingama kallon zaki iya shigowa, Tacinnu baki tace to ni mezan kalla anan, be kalletaba ma balle yasan tana yi, Tana shiga mai keke napep yaja sukabar wurin, basu tsaya ko ina ba sai wani gida, me adaidaita yayi parking, Dasauri jamila tajuyo tazuba ma dan liti ido, shima yajuyo yana kallonta!………. Heheheh chasssssss💃 Muje zuwa

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here