Home Instagram KAUYAN YAR KANDE HAUSA NOVEL

KAUYAN YAR KANDE HAUSA NOVEL

2
0

KAUYEN YAR KADDE
.
.
.
33-34
.
.

🅿3⃣3⃣➡3⃣4⃣

Jallabiya ya nema ya saka, ya saka kenan ta dawo cikin d’akin kallon ta yayi kamar yadda itama idon ta ke kan nasa, d’aga kai yayi alaman ya akayi ne, sai da ta ‘kariso ciki gab dashi sannan tace “ina kitchen d’in yake?” kallon ta yayi tare da cewa “kai Habibaty, kitchen d’in ne baki gani ba?, uhm,” nace ina kallon sa, don gaskiya bana gaji da kallon hasken idaniya ta.

“Muje na nuna miki tun kafin ki cinye ni da wad’an nan idanuwan naki” murmushi nayi ba tare da na bar kallon nasa ba.

“Muje nace, time na tafiya, gashi ko wanka banyi ba, kuma inason na le’ka asibiti da safen nan”.

“To muje” nace ina dawo wa kusa dashi, girgiza kai yayi tare da d’aga ‘kafan sa yafara tafiya, nima na fara.

Yana d’aga ‘kafa d’aya nima haka, waiga gefen daman sa da nake yayi yace “wai ni kakan kine baby?”.

” Kamar ya?” gaba yayi ba tare da ya bani ansa ba, ni kuma na bisa, kitchen d’in ya nuna min zai juya nace “mai za’a dafa maka?”.

” Abinda zaki iya ci, don da ganin wannan shafaffen cikin babu komai a cikin sa”.

“Hmmm, my heart kenan” kallo na yayi yana mai jin matsanancin farin cikin sunan da nakira sa dashi.

“Ina son ki” yace yana mai lumshe idanu wan sa, “nima haka” ba tare da na bud’e baki ba, lab’bana ne kawai suka motsa, kallon su yayi tare da jin wani irin yanayi.

Barin wurin yayi ni kuma nayi cikin kitchen d’in, tunani na fara “shin mai zan masa?” nai shiru ina nazari.

Ban iya kunna gas ba sai na kuna stove, d’aura ruwan zafi nayi, kafin yayi zafi na fere doya, yana tausa na juye, soya doya nayi da ‘kwai.

Ina gama wa na fito, lokacin shima ya fito a lokacin ya fito ‘kamshin shi ya cika ko ina na palon, ganin kallon da nake masa kamar wa wuya yasa ya saki wani had’ad’d’an murmushi.

Mayar masa nima nayi tare da nufo sa, cikin shagwa’ba nace lokacin da na iso gaban sa “gaskiya doctor kamin wayau” zaro ido da ya zama kamar al’adanshi yayi tare da min magana da ido, “name?”.

Turo baki nayi tare da cewa “kasani ma break fast bayan nayi wanka, kana ‘kamshi niko sai wari nake” nace ina shinshina jiki na.

Matsowa gab dani yayi yana murmushi tare da cewa “muji” yana kamo hannu na, tare da rankwafawa ya kai hancin sa a wuya na, yace “hunnnn, ‘kamshi, kinji ‘kamshin dakike kuwa baby?”.

Fincike wa nayi don nasan tsokana ta kawai yake, murmushin gefen baki yayi tare da cewa ” da gaske ‘kamshi kike, zo na’kara ji”.

Bibbiga ‘kafa na farayi a ‘kasa ina cewa “Allah ban wani ‘kamshi ni na sani, kuma ni wanaka zan sakeyi yanzu na fesa turaren ka”.

“Zo HAYATI, zo kinji” banza dashi nayi, shi kuma yana tsoron Allah yana tsoron abinda Joy za tayi.

Ko kallon sa banyi ba nayi hanyan d’akin sa “oh my god” yace tare da d’aura hannu aka, niko ina shiga nayi toilet d’in sa, wani irin ‘kamshi bayin yake, tu’bewa nayi na d’aura towel d’in sa, na fito da uniform d’ina a hannu palon na fito.

Jin motsina yayi tunani ko na fasa ne ya d’ago da kai don kallo na.

Da sauri ya kauda kai, murmushi nayi tare da mamakin sa, sai kace yaga wani abun tsoro.

“Ga uniform d’ina ka ninke min kafin na fito, yadda ba zai ya mutse ba” nace tare da ajewa kusa dashi.

Bai ce komai ba har nabar wurin, kuma ko sake kallo na baiyi ba.

Wanka na nake cikin nishad’i, da ruwa mai ‘kamshi, “nima yau zan zama ‘yar gayu” nace ina sakin murmushi.

Bayan na fito na ‘kwala masa kira don ba mirror bansan inda kayan ‘kamshin sa suke ba.

Yanaji ya kasa magana, don yana nan inda ta bar sa, a daskare yake don ko uniform d’in da tace ya nunke mata baiyi ba.

Sake ‘kwala masa kira nayi amma shiru babu ansa, don haka sai na fito tunani na ko ya fita ne, ina zuwa na gansa zaune inda na bar sa.

Cikin shagwa’ba na nufo sa, banyi wata wata ba na d’ane cinyan sa, d’ago da runannun idanuwan sa yayi tare da cewa cikin ma wuyacin hali.

Da sanyin murya “please kibar abinda kike, Allah addinin mu yahana haka, haramun ne abinda muke aika tawa, hakan zai kamu ga aika ta mummunan abu, ki bari kinji”.

” Ki adana su zuwa bayan auren mu” yace yana kauda kai, kallon sa nayi da mamaki, nace “meye abinda nake mara kyau?” shiru yayi bai ce komai ba.

Hannaye na nasa tare da juyo da fuskan sa, ina kallon cikin idon sa nace “meye laifin abinda nayi?, kaban ansa”.

Saka hannu sa yayi tare da zame hannu wana yace ” addinin mu ya haramta ke’bance war mu haka”.

‘Dage gira nayi tare da girgiza kai “to d’an d’agani please, kije kuma kisa kaya mu karya zaku makara fah, kalli” yace yana mai nuna min agogo.

Takwasa saura minti goma na gani, mi’kewa nayi tare da cewa “ina ka aje kayan ‘kamshin ka?” bai ce komai ba ya mi’ke, d’akin ya nufa nabi bayan sa.

Muna shiga ya mi’ka min wani jaka “gashi, please kiyi sauri muje” yace tare da fita bayan na ansa.

“My heart d’an kawo min uniform d’in” zuwa yayi bakin ‘kofa ba tare da ya d’aga labulen d’akin ba .

Yace “gashi” turo hannu sa kawai yayi, murmushi nayi ina mamakin wani irin addinine haka mai shegen ta kura?.

Saka kaya na nayi na fashe jikina da turarukan sa masu shegen ‘kamshi, amma abin takaici banji ‘kamshin kamar na jikin sa ba.

Fito wa nayi, kallon sa nayi tare da kallon break fast d’in bai ko ta’ba ba.

“Ya bakaci ba?” kallon na yayi tare da cewa “ke nake jira” ya tsina fuska nayi tare da cewa “kaci kawai na ‘koshi”.

Mi’kewa yayi ba tare da yace dani komai ba ya nufi ‘kofa, da mamaki na kira sunan sa.

Waigo wa yayi yana kallo na ba tare da ya ansa ba, ” bakaci ba “.

” Na ‘koshi ne nima” murmushi nayi tare da nufan inda yake tsaye, kamo hannu sa nayi .

Bai ce dani komai ba har na zaunar dashi, bud’e wa nayi tare da zuba wa a plat, na had’a masa tea duka nace “muci” tare da saka hannu.

Bai ce komai ba ya faraci, kad’an yaci yace ya ‘koshi tare da mi’kewa.

Nima na mi’ke, kallo na yayi tare da cewa “ci inajiran ki waje” .

“Na ‘koshi, kin tabbata? uhum”.

” Shikenan muje 8:10am har yayi ‘kila ‘kawan ki ta tafi” fita yayi na bisa a baya, ina fita ya saka key ya rufe ‘kofan.

Mukayo waje ya rufe gidan shima, rana ya fara fito wa mutane nata kai da dawo wa.

“Shiga kira ta” bace komai ba na nufi cikin gidan nasu.

Mama na tarar a tsakar gidan, gaishe ta nayi itako tana kallo na da mamaki a fuskan ta bata ansa min gaisuwan ba.

“Baku tafi ba?” tace, cewan ta haka ne ya ganar dani cewa Aisha ta tafi, don haka sai nai tsuru tsuru na kasa bata ansan tambayan ta.

“Joy dake nake fah” sosa ‘keya na farayi sai na dake tare da cewa “mantuwa nayi shine na dawo, to na duba d’akin mu ban gani ba shine na tuna jiya tazo ta ‘kar’ba, shine nazo duba wa”.

Shiru tana kallo na kamar bata yadda da abinda nace ba, sai daga baya tace ” me kenan?”.

“Litafin wata ‘yar class d’in mu, shiga ki duba, amma ai da kun dawo tare ta barki ke d’aya kin dawo”.

” Amma a mashin kika dawo ko?” tace ina gab da shiga d’akin.

“Uhum” nace kawai tare da sa kai.

Kallon d’akin na tsayayi kawai har kusan minti biyar sannan na fito, ganin bata tsakar gidan na saki ajiyan zuciya tare da falfalawa da gudu.

Ina fita na bud’e mota na fad’a cikin tare da sauke numfashi.

“Lafia?, ina ‘kawar taki?” yace yana kallo na.

Ban sa ansa ba nace “muje kawai” bai wani matsa ba ya tada mota muka bar wurin.

Mun fara nisa sannan nace “Aisha fa ta tafi, kuma nasan ta shiga gidan mu nema na”.

“Yayi, kinga mai himma kenan” turo baki nayi tare da cewa “naji ni ban da himma”.

” A’a ni bance ba” banza dashi nayi shima bai matsa ba ya cigaba da tafiyan sa.

Yana parking na bud’e ‘kofa zan fita, “ansa” yace .

Waigo wa nayi tare da kallon hannu sa, “ki ansa nace” hannu a dun’kule.

“Me zan ansa?” nace ina le’ka sa’kon hannu ‘kara dam’kewa yayi tare da sa d’aya hannu sa ya janyoni tare da kar’be jaka ta yasa min tare da saki na.

Zanyi magana yace “oyo wuce kin makara, maza aji kar a ta’ba min lafia jikin ki” murmushi nayi tare da fita daga motan.

‘Daga min hannu yayi nima haka nayi cikin makaranta.

Sauri ya tada motan yabar wurin bayan yaga shiga ta aji.

Ina shiga Aisha ta tsare ni da ido, murmushi nayi tare da cewa “lafia kallon malama?”.

“Ina kikaje ne besty? naje gida mama tace kin dad’e da fita”.

” Gidan doctor ” nace murya ‘kasa ‘kasa, don malam ya shigo lokacin.

Zaro ido tayi tare da bud’e baki, murmushi nayi tare da cewa gab da kunnin ta “rufe bakin, kinsan wannan malamin mai rainin wayau ne, ki bari sai ya fita sai ki sake wani tambayan”.

Aiko kamar wa wuya ta kasa magana rufe bakin tayi muka natsu aka fara darasi.

Yana fita Aisha ba ta barni na koda matsa ba ta jefomin tambayan.

“Mekikai a gidan doctor fisabilillahi da girman ki da ‘kiman ki?” .

“Tashin sa a barci nayi, bayan haka na masa break fast”.

San’kare wa tayi a wurin.

Niko dariya nayi, in banda abinki Aisha ina ruwan arne……..

**********

Rayuwa tama su Joy dad’i soyayya kawai suke kamar ba gobe, suna tsananin ‘kaunar junan su da kulawa da junan su
Sosai.

Amma fa Auwal bai sake sakacin barin ‘kofar gidan sa a bud’e ba, don yana tsoron Allah yana tsoron Joy.

Duk da haka bai tsira ba, a hakan tana yawan ta’ba sa, ko son shige masa jiki.

Wani abu da ta tsiro shine zuwa asibiti duk bayan ta dawo daga makaranta, sai tazo tawani kanai naye shi.

Haka suke ta tafiya har wa yau, yanzu haka saura jibi Auwal zai koma garin sa, ya gama sabis d’in sa, ya rasa yadda zai sanar mata.

Ganin cewa suna ta faman jarabwa, don bai son ya tada mata da hankali ko kad’an.

A haka har kwana uku tayi ba tare da yasan yadda zai ya gaya mata ba.

Can Abuja su mami sun kasa sun tsare suna jiran dawo wa Auwal shiru har washe gari bashi ba labarin sa.

Sun kira wayar sa a kashe, shiko yayi hakan ne saboda bai san mai zaice masu ba.

Sati d’aya da gama wan sa saura kwana biyu su Joy su gama jarabawa, yana zaune a ‘kofar gidan sa kawai sai hango motocin gidan su yayi guda biyu suna taho wa.

Farin cikin ganin ‘yan gida da fargaba suka taru suka diran masa a lokaci d’aya.

Mi’kewa yayi daga farin kujeran da yake zaune, dai-dai nan sukai parking, nufar motan sister d’in sa yayi.

Da farin ciki ya bud’e ‘kofar motan, ita ce hakin CE a bayan motan sai Akaram.

Ko bari ta fito baiyi ba yace “oyoyo sis, oyoyo my son”.

Harara ta maka masa, tare da cewa ” shiga mota muje” d’aure fuska yayi tare da cewa “kai Anty wani irin in shiga mota daga zuwan ki?”.

” Auwal ban wasa da kai nace ka shiga mota mu tafi” bud’e d’ayan motan da akayi ne yasa shi waiga wa.

Ba kowa bane illah Dady da kan sa, sai yaya wato Wanda ya kawo sa.

Ga farin ciki ga far gaba, amma hakan ya matse yayi musu barka da zuwa.

“Son mai kake a garin nan bayan ka gama abinda ya kawo ka?” cewan Dady ba tare da ya ansa sanu da zuwan da yake masa ba.

Shiru shima Auwal yayi, ganin zai ‘bata lokaci yasa Dady yace “shiga muje” rasa yadda zaiyi yayi tunda Dady da Kansa yace haka.

Kamar zai kuka yace “Dady kuje kawai gobe zan……….” bai ‘Kari saba sakamakon wani matsiya cin harara da Dady yayi masa.

Bai dan dara ba yace “Dady bari na had’a kaya sai muje”.

” Bama wani ka wuce muje” “akwai takadduna fa a cikin gidan”.

” Jeka maza rakasa” yace da yayan nasa, bai so hakan ba amma haka yayi gaba yayan yabi bayan sa zuwa cikin gidan.

Tarka ta takkdun yayi kaf tare da abubuwan sa masu mahimmanci suka fito, amma kafin su fito ya faki idon yayan ya rubuta leta ya aje a kan kujera d’aki .

Suna fito wa saka kayan a bot d’in motan yayi tare da kallon gidan yana mai jin wani iri a cikin ransa, gashi Joy suna makaranta yau bai san yadda ‘yar rigiman sa zatai ba.

“Dady bari na bawa gidan nan key d’in nazo”.

” Ga wani can bashi ya kai musu kana ‘bata min lokaci ” waiga inda dadyn yai nunin yayi.

Aiko ganin Muhusin ne yasamu kwanciya hankali.

Matsawa kusa dashi yayi tare da cewa cikin ‘kasa da murya yana mai tura masa abu a aljihu “‘kani na, don Allah ga wannan wayan da kye d’in nan Joy na dawo wa kaba ta, kace nace don Allah tayi ha’kuri zan zo bayan kwana biyu”.

” To yaya insha Allah zan gaya mata, yauwa ‘kanina nagode” yace tare da juyawa wurin motan .

Shigan sa keda wuya suka bar wurin………………..
.

To fah, wata sabuwa inji ‘yan caca🤨😅

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here