Yanda ake Dora photo akan Waka da wayar Android

YADDA ZAKU DORA PHOTO AKAN WAKA A WAYAR ANDROID . Kamar yadda kuke ganin wasu wakokin suna zuwa da photo akansu sai muyi mamaki idan mukaga hakan wato sai muga hotuna akan wakoki to wannan aikine na computer, to amma yanzu zamuyi bayanin yadda zaka dora photo akan waka batare da computer ba kawai ta hanyar amfani da wayar android . Abin babu wuya kawai kuyi download na wannan application mai suna . Tcm music tag editor.apk . Zaku iya download dinsa a playe store ko a google Bayan kayi download na wannan application saika budeshi da zarar ka bude zai kawoka inda wakokinsa suke to saika duba folder da suke saika za6i wakar da kake so ka sanyawa photo bayan ka zaba nan take zai kawoka wani shafi inda ananne zaka dora hoto Da sauran wasu gyare gyare da zakayiwa wakar kamar su sauya . . Title . Artist . Album . To idan zaka chanja ka lura da kyau daga gefan kowane Rubutu akwai inda aka Rubuta Fix to nan zaka danna sai kayi edit ka rubuta abin da kakeso Sannan daga kasa kuma zakaga photo da wakar tazo dashi shima daga gefansa zaka zakaga Fix saika danna nan nan take zata kawoka gallary dinka saika za6i hoton da kakeso ka dorawa wakar shikkenan da zarar ka xa6a zai dawo dakai kan app din inda kake aikin to saika duba sama zakaga inda aka Rubuta SAVE AND CLOSE shikkenan saika danna nan domin yin save bayan ka gama saika fita kaje ka duba wakar insha Allah zakaga wannan hoton daka dora ya hau shikkenan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *