Home Novels A TAUSAYAWA JUNA HAUSA NOVEL

A TAUSAYAWA JUNA HAUSA NOVEL

2
0

A TAUSAYAWA JUNA HAUSA NOVEL.

rik’e da wota bak’ar leda, Cikin hamzari da kulawa Aysha ta taryeshi hannu tasa ta karbi kayan hannushi sannan ta wuce gaba tare da cemai. “Barka da yammah Hamma”. Ajiyar zuciya ya sauk’e tare da zama can gefen ta kan 1 str ido ya lumshe tare da cewa. ” Alhamdulillah Aysha sai dai gsky yau kam akwai rana ga k’ishi gashi na biya cikin kasuwa na d’an saya miki takalmi da mayafi”. Sai kuma ya mik’a mata hannu alamar ta mik’o mai ledar, Cikin girmama wa ta mek’a mai tare da rabawa gefen shi ta zauna tana kallon ‘yan kayyayakin da ya sayo mata ta kalmin ya dauko ya zauna a kasa kan carpet ya zura mata takalmin cikin kula yace. “Wlh yayi miki kyau kinga yadda k’afarki ta gyara takalmin insha Allah inna samu kudi zan saya miki jakarsa ” Itama zamewan tayi ta zaune d’an nesa dashi cikin sanyi da tausayawa tace. “Hamma meyasa kake son kashe kud’i a banza da wofi ni ba yarin yaba ka rink’a kashe min kudi yanzu ba da safe kake cewa ba kudi a hannun kaba kuma shine daga samo su ka saya min wannan tarka cen meyasa bazamuyi tattali ba?”. Kai ya jinjina cikin jin dad’i yace. ” Aysha Allah ya miki albarka Ngd da tausaya sarki gareni amman kibar korafi kar ina kashe miki kud’i dan kuwa Aysha duk wani namijin kirki toh burinsa ya faran tawa matar sa da yaran sa muddin kikaga ba’ayiba toh ba’asamu damar yi bane inko haka ta faru sai *A tausayawa juna* d’an ba Wanda zaiso yaga iyalanshi a k’askance sai dai in abin yafi karfi kinga ko tunda na samu dole namiki tunda dama nauyi nane ai ko matata?”. Murmushi tayi cikin farin ciki tace. “Allah ya saka da alkhari ubangiji yaa jibanci lamuran ka Allahu rabbi ya karama arzik’i da wadata Allah ya had’aka da halal d’inka ubangiji ya rabaka da haram Ngd Ngd Ngd Hamma na” Gdy take mai cikin farin ciki da ganin girman kyautar da ya mata, Cikin jin dad’in halin matar tasa yace. “Nifa kin San ban son wannan godiyar kinsan irin godiyar da nake so yanzu kuma muna cikin watan Ramadan ne kuma da ranane dan haka Adana godiyar sai anjima in munsha ruwa”. Murmushi kawai tayi tare da tattara kayan sannan tayi cikin d’aki bayan ansha ruwa ne ya tafi masallaci itako tai tata sallan tare da kara kimtsa gida. Suna rayuwar su cikin rufin asiri da tausayawa juna duk k’ank’antar abinda ya mata ita ganin shi take da girma da daraya…. *Gidan ya Umar,da Maryam da y’an yaran su Umar yayan Rukayyat ce kuwa 1 uba 1* Tun 5 dai-dai Maryam ta gama aikinta gudu-gudu sauri-sauri da tsoron kar ya Umar ya dawo ya samu bata gama ba dan shi Umar mutunne mai gaggawa da rashin uzuri gashi, Shi har kullum gani yake aikin cikin gida ba wuya sai dai in mace nada saib’ine, sam Maryam bata rasa komaiba najin dad’in rayuwa ita da yaran ta sai tausaya warsa da yimusu uzuri suka rasa. 6:00 pm ya shigo cikin gidan cikin sauri Maryam ta taryeshi tare da cewa. ” Sannu da hanya Ya Umar”. Aha yace ba tare da ya tsaya ba sai Leda da ya mik’a mata cikin d’an d’aga murya yace. “Kajine ki min gashi nan mai d’an romo-romon nan kiyi sauri fa kinga ankusa kiran sallah”. Ido ta zuba mai cikin binshi a baya a hankali tace. ” Ya Umar saura minti 25 nefa a kira sallah kuma yau jiri na wuni dashi da ker nai aikin ma wlh banda lfy”. Cikin fushi ya juyo ya kalleta tare da cewa. “Wlh ke dai kin fiye saibin tsiya mene a cikin aikin gidan nan naga dai akwai mai wonke-wonke da shara da wonki, girki nefa kad’ai aikin ki amman duk sai ki wani sakewa dan son jiki”. Sai kuma ya juya ya kalli ‘yarsu karama da yanzu ta tashi daga bacci shiyasa kanta dake d’an tubke akan gobe za’ kaita kitse. Cikin tab’e fuska yace. ” kalli kan Ikram fa kin barta kai a tsefe ba kitso”. .sai kuma ya d’an rink’a lek’a cikin gidan da parlon dan neman ta ina zai cita gyara, Ganin babu kuma baki ya saba mita sai cewa yayi . “Fito min da kayan da zansa ina fito wonka sannan kuma kije ki gasamin naman nan ki kuma kitsewa ikram kantan nan”. Inda sabo Maryam Ta saba da wannan rashin tausayawar daga gun mijin nata bawai kuma son tane baiyi ba a a kawai dai baida bawa mace uzurine shi gani yake me aikin mace ai duk aikin kamar wasane. Kayan ta fara cire mai San nan ta sawa ikram hula a kanta sai kuma ta wuce kitchen ta fara aikin ana kiranbsallah tazo ta had’a mai komi sannan ita kam ta d’an cin dabino sai kuma tayi sallah sannan ta koma kitchen din, shiko yana dawowa masallaci ya shiga parlon ya samu su ikram da yayun ta suna wasa cikin daga murya yace. ” kai Isma,il ina Mamin Ku?”. da sauri yace . “Daddy Mami tana kitchen ko ruwa bata shaba”. Murmushi ya d’anyi sannan yace. ” Isma,iI Mamin Ku saibin ta yayi yawane nima yanzu yunwa nakeji amman kaga na kasa samun kulawar ta”. Da sauri yaro yace. “Toh Daddy bari na sama Abin cin ko?”. Kai ya gyada tare da cewa “toh ya zanyi ai ya zamemin dole zo kaida Sultan muci” Haka suka zauna sunaci yana ta mita, Ita kuma sauri-sauri ta gama sannan tazo ta kawo musu kafin nan isha tayi sai kuma tayi sallah sannan ta kimtsa parlon tazo tawa yara wonka sukaje suka konta shima taje ta kimtsa shi sannan ta juya zata fita taje taci abinci tai wonka ta samu ta konta ta huta sai kuma tajishi yana. “Maryama zo mana ina kuma zakije”.


Cikin rawan murya tace. ” ruwa zanje insha kuma zanyi wonka gashi bacci nakeji”. Cikin rashin damuwa yace . “Toh kiyi da sauri ina jiran ki”. Kai kawai ta gyada sannan ta fita tana mai jin zafin rashin tausayawar da mijin ta ke nuna mata . *Gidan ya Umar kenan* *Koya gidan Bashir kuma ke ciki* Rukayyat ce biye dashi a baya cikin ya mutsa fuska da tura baki tace….. *Masu karatu wanna lbrin d’an gun tune kuma nayishi kan A tausayawa juna kuma ayiwa juna uzuri mussaman a wannan marran da muke ciki mata mu tausayawa mazanmu kan samunsu da rashin su mu kasance masu godiya da abinda zasu mana duk k’ank’antar Sa mu gajarca buri da son abin duniya. lbrin 3 pages ne koma 2*

gatan da zai samarwa mace na banzane matuk’an bai sama mata kulansa da tausayawar saba”. Cikin sanyi murya da d’an kuka tabawa Rukayyat lbrin irin zaman da take da ya Umar d’in, Sosai jikin Rukayyat yayi sanyi watoh abinda take ganin shirme ne Bashir ke mata ase shine babban farin cikin ma’aurata gashi rashin sa yasa Maryam zubda k’ollah duk da daular da take ciki”. Sai kuma ta kauda tunanin tare da cewa. “Ke taki matsalar me sauk’i ce tunda baku rasa komai ba nifa Bashir bama sanin akonsa da babunshi sai dai kaga yanawa mak’ota da mabarata”. Nan ta basu lbrin irin rigimar da suke a yan kwana kinnan. Ajiyar zuciya Maryam tayi tare da cewa ” wlh ke Rukayyat dad’ine ya miki yawa Ni in nice na samu irin kulawar da Bashir ke baki ai bani da wani bak’in ciki, Rukayyat kiji tsoron Allah fa yanzu ke da me Bashir ya regeku keda yaranki”. Shiru Aysha kam tayi tana mai zuba musu ido cikin sanyi dason tunasar dasu ta gyara zama tare da cewa..

Da forko dai zance daku abin da kukayi bakuwa mazan ku a dalci ba dan wannan sirri ne wanda ke tsakanin ku sirrin mazan Ku ne sirrin gidajen kune bai kamata ku fito kuna tad’ashi a anguwa ba, Tabbas ba abin da zance dake Maryam sai dai nace dake Allah ya baki ladan hakurin da kikeyi kuma Allah ya fahim tar da mijin ki rabbi ya samai tausayin ki cikin ransa, dan hak’ik’a rashin tausayawa juna da wasu maza ke gwada matan su yana jawo rashin ji tuwa”. Shiru Maryam kam tayi cikin jin sanyi na ratsata a ranta duk zafin da take k’unshe dashi ya fara tafiya a ranta kuwa godewa Allah take da ya had’ata da Aysha k’awar kirki k’awar mutunci da amana k’awarda dake bid’ar a gudu tare a tsira tare dan da wata ce sai dai ta ingi zata, Cikin sanyi murya tace. ” Aysha ngd da tuna sarwa insha Allah zan ke tsare sirrin gidan aurena zanke Addu’a Allah ya fahimtar da ya Umar “. Murmushi tayi cikin juyawa gun Rukayyat ta kafeta da ido cikin yanayin kinban mmk kin kuwa ji kunya har gaban Allah, ta bud’e baki zatayi mgn kenan, Rukayyat ta katseta cikin yin k’asa da murya gudun kar Innarta ta jisu a hankali tace. ” Ke Aysha na fahim ci bazaki gane abin da nakeji ba dan ke komai a wadace kike samun shi shiyasa kike gani kamar wani mugun abu nakeyi, ita ma Maryam dan matsalar ta k’arama ce shiyasa bai damun ta sosai”. Cikin d’an d’aga murya Aysha ta fara mgn don so take Innah ta jisu tunda ta fahimci Rukayyat na tsoron Innar taji takuma gano duk tsiyar da takewa Bashir Innah bata saniba dan da ta d’au mataki cikin tsareta da ido tace. “Rukayyat kiji tsoron Allah, ki tuba ki komawa Allah ki sani abin da kikeyi kina sabawa dokokin Allah kisa a ranki shi aure ibadane ki d’aukeshi a matsayin bautar ubangiji ki cirewa ranki cewa shi Aure sharholi ce ki dena d’aukan gidan Aure wurin shanawa ne kisa a ranki aljannarki kike farau towa, Rukayyat wlh ki nemi gafarar mijin ki tun kan lkcin ya k’ure miki kinfi kowa sanin kina cutar da zuciyar mijinki da mugayen kala manki , Shin wai Rukayyat ina ilimin ki ya tafi shin kin manta ita wannan duniyar ba komai cikin ta sai rud’u. Shin ko Mataa wul hayat ke rud’an ki?, toh inma shine ki sani rayuwar k’ele-k’elen duniyar nan ba ma dauwami bane ki sani k’ele -k’elen k’alilan ne, kin tuna cewa dama ita wuta an kewaye tane da ababen k’awa da more rayuwa da sharholiya, ita kuma aljannah an kewaye tane da abin da rai zaike ganin takura ne, Rukayyat shi haram sauk’in aikata wane gareshi shiko hakuri rahama ne a rayuwar duniya data k’iyama”. Hannu tasa ta dafa kafad’ar Rukayyat cikin sanyi tace. ” Rukayyat ko kin mata gidan Annabin muma Abin koyinmu akwai lkcin rayuwa tai musu tsanani har ta kai saida akayi kwana 3 basu d’aura tukunyar girkiba, kinyi karatu kinsan yadda a wannan lkcin matan sa d’in suke hakuri da godewa Allah da wannan jarraba war, Amman wai ke da bakiyi koda wuni d’aya bakiyi girkiba wai a hakan kike gaza hakuri da tausayawa ga mijin ki, Shin da kike cewa batun kayan sallah da k’ele k’ele shin ki tuna matan Annabinmu abin koyinmu a lkcin da su suke ganin a matsaya yinsu na matan shugaba amman basu da kayayyakin k’awa na rayuwa har suka tinkari Annabinmu da buk’atun su a lkcin da suka buk’aci kayan duniya na jin dad’i, suka saka shi a gaba kan dole sai ya samo musu, da ranshi ya baci, sai yayi musu yaji na tsawon wata d’aya watau kwanaki ashirin da tara 29, Amman saboda halin mata sai a hankali yana shigowa gida sai ya fara had’uwa da Nana Aisha (A.S), tana ganin shi sai tace. “Ba kace wata d’aya zakayi ba ai kwana 29 ne yau, alhalin kuma a ranta tayi kewarsa fa tana Allah Allah ya dawo, shi kuma lokacin ya k’osa ya dawo wajen matan shi shima , sai kuma ga abinda tayi mai welcome da shi. sai yace “mata ai kwana watan musulunci 29 ne sai tace toh. Daga baya kuma sai Allah ya sauk’ar da Ayoyi akan cewa idon suna son jin dad’in duniya ne toh su fad’awa Annabi (S.A.W) d’in zai sake su saki kekkyawa suje su sami abinda sukeso, idon kuwa sun zabi Manson Allah (S.A.W) suyi hakurin zama a ko wanne hali da shi, toh lallai Allah ya tanadar musu lada ninki biyu fiye da sauran matan duniya gaba d’aya, sa’ sannan kuma zai basu fiyayyen al’jannah tare manzon shi. sai sukace sun zabi Allah da manzon shi kuma kafin hakan ma Allah yace in sun zabi rabuwa da Annabin toh Allah zai musanya mishi da wasu matan da suka fisu a komai, wad’anda kuma bazasu sakashi ciwon kai ba. a cikin suratul tahreem”. A hankali Rukayyat ta rink’a siyayar da hawaye a fuskarta cikin tsoron da nadamar abin da tayi tayiwa mijin ta sosai taji tsoro ya rufeta ya zatayi da hak’k’in mijin ta da bata mai da tayi tayi shin in tajawa kanta saki koya makomar ta zata kasan ce shi kuwa ta tabbata Allah zai musanya mai da mai rufa mai asiri ko dan hakuri da yayi tayi da ita, Cikin kula ta rik’e hannun Aysha tare da cewa “ngd Aysha Allah ya saka da alkhairi ngd da tuna tarwa”. kai ta jinji cikin sanyi tace “ba komai Rukayyat yiwa kaine” Cikin mmk suka d’ago Kansu suna kallon Innah da ta shigo tare da cewa..

Cikin sanyi Innah ta zauna gefen su tare da cewa. “Hak’ik’a Aysha kin cika k’awa ta gari mai tunatar wa tabbas ke abin son kiyi k’awance ga duk mai hali irin na Rukayyat dan zaki tunasar da ita hak’ik’a naji dad’in kasan cewarki tare da y’ata da surkata”. Sai ta kuma juyawa gun Maryam da tayi k’asa da kanta cikin kula da k’aunar matar d’an nata tace. ” Maryama Allah ya miki albarka rabbi ya baki ladan hakurin da kikeyi, kuma Insha Allah Umar kam zai sauya miki insha Allah zanmi shi nasiha zan kuma nusarda dashi zan fahimtar dashi illar rashin tausayawarsa gareki”. Cikin sanyi tace. “Innah kar ayi mai fad’a zai d’auka k’ararsa na kawo”. Murmushi tayi tare da juyawa gun Rukayyat cikin had’e fuska tace. ” kinga mata nagari sune masu hakuri da mazan su a cikin ko wanne yanayin matukar bai sama addininmu ba, kinga duk yadda yake mata tana gudun bacin ransa”. Cikin sanyi tace “Innah Insha Allah nima zan kula zan nemi gafarar Abban Salim hak’ik’a nasan yayi hakuri dani da halina”. Innah ce taci gaba da cewa . ” Hak’ik’a ya zama wajibi a garemu mata mu tausayawa mazanmu domin suna buk’atar tausayawar mu garesu sabida rayuwa ta juya komai ya canza Allah ya kawomu lkcin da tsada tai mana kaka gida sai dai muyi ta Addu’a Allah ya kawo mana d’auki dan wannan tsad’a ba mutun d’aya ta shafaba ta shafi kowa, Kuma wannan tsada ba laifin kowa bane muk’addari ne jarrabawa ce mu dage mu samu muci wannan jarabawah, sannan mu godewa Allah da ya bamu zaman lfy a kasar dan zama lfy yafi zama d’an sarki, Mata musa hakuri a ranmu muke godewa mazanmu da duk abinda sukayi mana komai k’ank’antar sa, zanin sallah ba wajibi bane sai Super was ba kuma ba sai Holland ba dan super tafi k’arfin mai k’aramin k’arfi abin dubu 25 ya koma dubu 42 yayin da duk sauran zannuwan suka ninka kud’insu, shin maza suji da ciyar damu ko da burukan rayuwar mu abincin kanshi sai hamdala ba batun araha kam daga kan maggin da da d’ari 200 zuwa yanzu yaje har d’ari 400 sauran kayan masaru finma komai yayi wuta bare aje ga kayan yaran da sai dai hamdala babban gatan da Allah ya mana dai mun samu zaman lfy, dako da arahar Amman baka da konciyar hankali da zaka samu nitsuwa ana rayuwa ne cikin tsoron da firgici ga dukiyar da abin more rayuwar amman ba nitsuwar da konciyar hankalin da za’a mori arahar haka ko wanne shekara da yadda zai zoma bani ‘Adam mu godewa Allah mu daina jingina tsadae da muke ciki akan wani abokin halitta kamar mu wanda bai da damar sau k’ak’awa ko tsanan tawa mukoma ga Allah mu dena al’k’anta tsadar damuke ciki akan shugaban mu Baba Buhara ba Allah bane ba kuma ba manzon Allah baneba kuma ba kumfa yakun neba shima Bawane kamar kowa baida ikon sauk’ak’awa ko tsanan tawa”. Sosai tai tamusu nasiha mai rasa jiki daga bisani tajuya gun Aysha tai ta mata Addu’a sannan ta baiwa Maryam hakuri ta kuma tasa Rukayyat a gaba tai ta mata nasiha. sannan suka fito parlon suna fita Aysha tace ita kam zata tafi aikin yamma najiran ta suna cikin haka Bashir yazo d’au kar Rukayyat ganin Aysha zata fita sai suka tafi tare ya sauk’eta a k’ofar gidan ta sannan ya juya da Rukayyat kuma ya nufi gida da ita, tun an cikin mota Bashir ido ya zuba mata ganin duk jikinta a mace ga fuskarta data nuna alamar tayi kuka gaba d’aya sai abin ya dameshi cikin kula yace. “Baby meke damun ki? ko azumin ne ke wahal dake?”. jiki a mace ta tsura mai ido tana mmkin yadda Bashir ke tausaya mata Amman ita ta kasa mai uzuri a rayuwar su, shiko ganin tayi shiru yasa d’aya sauk’eta ma bai fitaba sai bin bayan ta yayi suna shiga parlon ya kalleta cikin sanyi yace. ” Baki da lfy ko?” kai ta girgiza alamar a,a Ayijar zuciya ya sauk’e tare da cewa . “OK ki konta ki huta toh bari na shiga kitchen na fara mana aikin kafin su Salima su taso islamiya na d’auko su”. yana kaiwa nan ya nufi kitchen ita kam sai binshi da ido tayi cikin mutuwar jiki tana son mishi mgn da Bashir hakuri da nemar yafiyar sa sai kunya ta hanata a haka har zuwa dare. Bayan sun gama komai har Bashir ya konta itako tana gefen shi tana zaune mik’ewa yayi cikin sanyi yace. ” Na manta abu a moto bari na d’auko”. Har ya mik’e sai ya kuma zama jin ta rik’o hannushi cikin sanyi da kunya murya a raunane tace. “Abban Salim ka gafar ceni kamin afuwa hak’ik’a nasan na kasance mai b’atama da kalamai na masu zafi da d’aci, Hamma Bashir ina tsoron me zancewa maliccina in namutu da hak’k’in ka, ka yafe min hak’ik’a na gane kuskure na na kasa tawausaya ma bare nama uzuri”. Sai ta kuma fad’a jikinshi tare da sakin kukan nadama, cikin sanyi da jin dad’i ya tsura mata ido tare da sauk’e ajiyar zuciya yace. ” Share hawayen ki matata ni dama ban rik’eki ba na yafe miki duniya da lahira Allah ya miki albarka Baby na”. Haka suka rink’a farin ciki da samun nishad’i cikin sauri Bashir ya fice yana “bari kiga wani abu” Bayan ya dawo ne ya dire kayan hannushi kayan yaran masu kyau da tsada kala uku-uku na mata da maza sai turame 2da leshi 1 sai shadda mai kyau kala 3 sai sauran tarka cen yara su takal ma yan kunne gyale da dai sauran su cikin mmk Rukayyat ta bishi da ido, Shi kuma fuska a sake ganin ya samu lfy a gun matar tasa yace. “Ga kayan yaranki Hajia kema ga naji nima ga nawa sannan naki zaki d’inka da Salima niko zan d’inka da salim kinga d’en sun samu kala shida -shida ko?”. Kai ta sunkuyar cikin jin kunya da nadama ta fad’a gareshi gashi da batayi mgn bama da ba taji kunya a banza ba. Haka rayuwa ta koma musu cikin wadatar zuciya da tausayawa juna da yiwa juna uzuri shi kam Bashir Allah ya Bashir ladan hakurin shi….. Maryam ce konce tana baccin ta cikin sanyi taji Umar na Jan yatsun k’afar ta a hankali ta bud’e ido tana kallonshi shiko murmushi yayi cikin sanyi yace. ” Baby tashi muyi sahur kada mu makara”. ido ta lumshe tare da cewa. “Ni bacci nake ji Ya Umar kuma nagaji”. da sauri ya mik’e tare da cewa bari na kawo miki abin cin nasan kin gaji kina k’ok’ari ga Ramadan ga aiyuka sun k’aru”. Abin cin ya kawo har gaban ta sannan ya had’a mata tea da kanshi ya bata. Ita kam Maryam Allah take godewa d’aya canza mata halin mijin ta. Yusuf da Aysha ko rayuwa ta kara musu dad’i cikin fahim tar juna.


 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here